
Gwamnatin jihar Zamfara ta rufe ofisoshin gidan talabijin na NTA da Pride FM da Gamji TV da kuma Al’umma TV a jihar sabo da sun ɗauki taron siyasar ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dauda Lawal.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa taron ya gudana ne a jiya Asabar a gidan dan takarar jam’iyyar PDP da ke hanyar Gusau GRA-Ring Road.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya sanar da hakan a gidan rediyon jihar a yammacin jiya Asabar.
Gwamnatin ta kuma umurci kwamishinan ƴan sandan jihar, Yusuf Kolo, da ya kamo duk ƴan jaridar da su ka halarci taron.
Duk da cewa Dosara bai bayyana dalilan rufe tashoshin ba, amma majiya mai tushe ta ce dalilin ba zai rasa nasaba da yadda gidajen jaridar su ka watsa taron na Lawal kai tsaye ba.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, a ranar Juma’a ne gwamnatin jihar ta sanar da cewa za a rufe dukkanin kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi, biyo bayan sake barkewar hare-haren ‘yan bindiga a kan al’umma.
Gwamnatin ta kuma bayar da umarnin dakatar da duk wani taro da ayyukan jam’iyyar APC cikin gaggawa a matsayin wani bangare na damuwa da tausayawa gwamnatinsa ga mutanen da abin ya shafa.