
Ambrose Akinmoluwayan da matarsa na cikin halin farin ciki sakamakon kyautar da Ubangiji ya basu ta ƴan-biyu, bayan sun shafe shekaru 16 da aure amma ba su samu haihuwa ba.
Ma’auratan sun bayyana hakan ne ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a wani taron addu’a ga ƙasa da shugabanni wata coci ta shirya a Abuja.
NAN ya rawaito cewa an sadaukar da tagwayen; Joseph da Joshua, ga Ubangiji a yayin taron addu’ar, wanda matar babban limamin cocin, Dr Adeola Ilechukwu ta shirya.
Jim kadan bayan sadaukarwar, Akinmoluwayan ya shaida wa NAN cewa ya auri matarsa Mercy ne a ranar 3 ga Disamba, 2005 a jihar Ondo.
“Na yi aure a cocin Charismatic Renewal Ministries da ke garin Ondo.
“Na yi aure da matata, Mercy Adenugba, wacce a yanzu ita ce Mercy Akinmoluwayan,” in ji shi.
Mijin, wanda ya ce zai cika shekaru 52 a ranar 23 ga watan Janairu, ya ce sun dauki shekaru 16 kafin su samu kyautar Ubangiji.
“A wannan shekara, 12 ga Agusta, matata ta cika shekaru 50. Mun haifi jariran a ranar 27 ga Satumba, 2021 a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Abuja,” in ji shi.
Ya ce ko da ya ke akwai ƙalubale na jiran tsammani, “domin mu Kiristoci ne kuma mun yanke shawara da yardar Ubangiji cewa za mu yi aiki wajen sanya wannan aure namu ya daɗe, ba mu ƙyale wahala nan da can ta yi wa zamantakewar mu illa ba. ”
A cewarsa, muna sa ran Ubangiji Ya ba mu ƴaƴa, inda ya ƙara da cewa “amma ko da ba mu samu ba, mun kuduri aniyar cewa ba za mu tsinke igiyar aurenmu ba.”