
A jiya Talata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya yi alkawarin ɗora wa daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dora wajen tafiyar da gwamnatin da za ta inganta tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar, idan aka zabe shi a zaben badi.
Ya ce aiwatar da manufofin ci gaba na jam’iyya mai mulki zai karfafa hadin kan kasa, tabbatar da ci gaba da kuma baiwa ƴan Nijeriya fahimtar kishin kasa.
Tinubu, wanda ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan nasarorin da ya samu, ya kuma yi alkawarin inganta abubuwan da gwamnati ta gada a sassan kasar nan.
Tinubu ya yi magana ne a kan taken: ‘Habaka Tsaro, Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Sauya Tattalin Arziki’ a taron bita ga Ministoci da Sakatarorin dindindin a Abuja.
Tinubu ya ce: “ Shugaban kasa da sauran membobin gwamnati, zan iya cewa: Idan aka zabe ni, zan ba da girmamawar da ta dace ga kokarinku da abin da kuka gada. Zan yi aiki a cikin ruhin hadin kai, manufa ta kasa wacce ta sanar da kafa jam’iyyarmu tare da bayyana ayyukan gwamnatin ku.