Home Labarai Ƴan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga masu zanga-zangar EndSars a Lekki

Ƴan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga masu zanga-zangar EndSars a Lekki

0
Ƴan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga masu zanga-zangar EndSars a Lekki

 

Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Legas sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da a halin yanzu suke gudanar da ita domin nuna jimamin shekaru biyu da kisan da su ke zargin an yi wa ƴan uwansu a Kofar Lekki da ke jihar Legas.

Masu zanga-zangar da a halin yanzu ke yin tattaki a kan kofar a wani bangare na bukukuwan tuna wa da zagayowar ranar, an ce sun yi arangama ƴan sandan da ke ɗauke da makamai da aka tura domin kare tarzoma.

Fitattun jarumai da suka hada da Folarin Falana, mawakin Najeriya da aka fi sani da Falz ne su ka jagoranci wannan fitar a a yau Alhamis.

A cewar sanarwar da aka raba wa manema labarai, motocin da ke jerin gwanon za su bi ta kofar karbar haraji, suna ɗaga tutocin Nijeriya tare da rera taken #EndSARS.