Home Kasuwanci An ɓullo da sabuwar hanyar shawo kan ƙarancin abinci a Nijeriya

An ɓullo da sabuwar hanyar shawo kan ƙarancin abinci a Nijeriya

0
An ɓullo da sabuwar hanyar shawo kan ƙarancin abinci a Nijeriya
A ci gaba da ƙoƙarin shawo kan matsalar ƙarancin abinci a ƙasar nan, masu ruwa da tsaki a fannin noma sun ɗauki gaɓaran shawo kan matsalar.
Kungiyar Manoma ta Ƙasa, AFAN, da Tingo Mobile Plc, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar domin samar da kayayyakin amfanin gona,kayan aikin gona da na’urorin tafi da gidanka ga manoma don taimakawa wajen inganta amfanin gona da sauƙaka samun masu saye.
Yarjejeniyar, MOU wadda aka sanya wa hannu a jiya Laraba a Abuja, za ta baiwa kamfanin Tingo Mobile Plc damar samar da kayayyakin noma kamar irin su iri, taki, tarakta, sinadarai, da lamuni ga mambobin kungiyar AFAN, wadda ta yaɗu a ɗaukacin jihohin ƙasar nan 36.
Domin taimakawa samar da abinci
Baya ga kayan aikin noma, Tingo zai kuma samar da na’urori masu inganci don tallafa wa ƙananan manoma da nufin sauƙaka shiga kasuwanni don sayar da amfanin gonakinsu.
Da yake jawabi yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Shugaban ƙungiyar Tingo, Chris Cleverly yace an gudanar da wannan cigaba ne da nufin magance matsalolin ƙarancin abinci a Nijeriya, inda ya ƙara da cewa akwai buƙatar a tallafawa manoman karkara da tsare-tsare da za su bunƙasa amfanin gonakinsu.
A cewarsa, cigaban zai kuma magance rashin aikin yi tare da baiwa ƙananan manoma damar ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban tattalin arziki ƙasar.
“Tingo Incorporated babban kamfani ne na Agri-Fintech, tare da jarin kasuwa sama da dala biliyan 2, wanda shekaru da yawa yana canza al’ummomin karkara,” in ji shi
Shima da yake nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar ta AFAN, Dr Farouk Rabiu Mudi ya bayyana cewa shigar da ƙungiyoyi masu zaman kansu wajen magance kalubalen da manoma ke fuskanta ya kasance mai ma’ana.
Ya bayyana cewa sabuwar yarjejeniyar zata ba manoma dama a duk faɗin ƙananan hukumomin ƙasar nan domin inganta amfanin gonakinsu.
Mudi wanda ya ƙara da cewa yarjejeniyar sulhu da Tingo abin farin ciki ne, musamman a daidai lokacin da manoma ke kirga asara daga ambaliya.