
Kamfanin lemo na Maltina ya ƙaddamar da wani sabon talla na telebijin mai taken “Bikin Masarauta”.
Hakazalika kamfanin ya ƙaddamar da wani kamfe mai taken “Da Maltina Za mu samun Haɗin kai da Farin ciki”.
An yi bikin ƙaddamarwar ne a kasuwar Ado Bayero Mall a jihar Kano a ranar Alhamis.

Da ya ke jawabi a wajen taron, wani Manaja a kamfanin, Elohor Awe-Olumide ya ce kamfanin ya fahimci cewa babu wata kyauta da ta wuce samun farin ciki tsakanin ƴan uwa da abokan arziki.
A cewar sa, burin Maltina shine ta faranta wa al’umma, musamman a wannan mawuyacin hali da a ke fama da shi, inda ya ƙara da cewa shi yasa kamfanin ya kirkiri wannan kamfe ɗin.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ƙaddamar da sabon tallan, wanda aka haska a majigi, ya faranta wa mahalarta taron.
Bayan haka, fitattun jaruman masana’antar Kannywood da Nollywood, kamar su Rahma Sadau, Tomike Adeoye da Osas Ighodaro, har da ma mawaƙi M. I. Abaga sun nishaɗantar da mahalarta taron.