
A yau Alhamis ne wata kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wata mata da ake zargi da kashe mijinta a ruwa a shekarar 2019.
Saurayin nata da abokin aikata laifin nasa kuma an yanke musu hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari.
Kotun gundumar Incheon ta yanke hukuncin ne ga Lee Eun-hae, mai shekaru 31 da kuma saurayinta, Cho Hyun-soo, mai shekaru 30, tare da ba da umarnin su sanya na’urar bin diddigi a jikinsu tsawon shekaru 20 bayan cika shekarun da aka yanke musu.
An tuhumi mutanen biyu ne da laifin tursasa mijin matar mai shekaru 39 da haihuwa da ya faɗa cikin wani kogi mai zurfi a Gapyeong, mai tazarar kilomita 60 daga gabashin Seoul, a watan Yunin 2019, duk da cewa bai iya ruwa ba, lamarin da ya sanya ya nutse a ruwa ya mutu.
An kuma zargi mutanen biyu da yunkurin kashe mijin a waccan shekarar ta hanyar sanya masa guba a watan Fabrairu da kuma kokarin nutsar da shi a wurin kamun kifi a watan Mayu.
Tun da farko dai masu gabatar da kara sun bukaci daurin rai-da-rai ga duka biyun bisa ga cewa sun shirya kisan ne tare.