Home Siyasa Ƙungiya ta roƙi ƴan Nijeriya da su dena bari ƴan siyasa na siye su da kuɗi

Ƙungiya ta roƙi ƴan Nijeriya da su dena bari ƴan siyasa na siye su da kuɗi

0
Ƙungiya ta roƙi ƴan Nijeriya da su dena bari ƴan siyasa na siye su da kuɗi

 

Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna ‘Godspeed Leadership and Mentorship Development Initiative’, GLEMDI, a yau Juma’a, ta buƙaci ƴan Nijeriya da su dena bari ƴan siyasa na siye su da kuɗi, inda ta buƙaci su zaɓi shugabanni da za su magance matsalolin ƙasa.

Ene Okwulu, Jami’ar Fasahar Sadarwa ta GLEMDI ta bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, a Abuja.

A cewar Miss Okwulu, dole ƴan ƙasa su ɗauki laifin sake zaɓar baragurbin shugabanni a duk lokacin zaɓe tsawon shekaru sabo da kin fito wa su ma a dama da su.

“Mun ga gazawar shugabanci iri-iri, matsalolin tattalin arziki da cin zarafi na siyasa, amma duk da haka ƴan ƙasa ba su fahimci cewa su na da karfin sauke shugabanni baragurbi ba.

“An faru samun ci gaba sabo da mun fara ganin canji kadan-kadan musman ta yadda a ke fita sosai a yanki katin zaɓe, karɓar katunan zabe, samun ilimin siyasa da inganta tsarin zabe da dai sauransu.

“Dole ne ƴan ƙasa su farka su san abubuwan da ke kokarin gurɓata musu tunaninsu.

“shinkafa, garri da sauran kayan masarufi ne da ƴan siyasa ke raba wa lokacin zaɓe ya zama kamar cin mutunci ne ga hankalinmu da tunanin mu, inda da ga an gama zaɓe, sai mu neme su mu rasa,” in ji ta.

A cewar Miss Okwulu, Nijeriya ta fada cikin matsalar rashin tsaro da ke shafar tattalin arzikinta, yayin da ƙasar ke fuskantar kalubale na cin hanci da rashawa, ilimi da rashin aikin yi da dai sauransu.