
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babban bankin Najeriya CBN ya samu goyon bayan sa wajen shirin sauya fasalin takardar Naira a watan Disamba.
Maitaimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a Abuja a jiya Lahadi cewa Buhari ya bayyana matsayar sa yayin da ya ke magana a wani shirin gidan rediyon Hausa da za a yaɗa shi gidajen rediyo a jibi Laraba.
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta shaida wa kwamitin majalisar dattawa a ranar Juma’a cewa CBN ba ta tuntuɓi ma’aikatarta ba a shirinta na sake fasalin Naira da fitar da sabbin kudade.
Misis Ahmed ta zargi tsarin da cewa bai dace da halin da ake ciki yanzu ba.
Sai dai Buhari ya ce yana da yakinin cewa al’ummar kasar za su samu riba mai yawa da matakin da CBN ya dauka na sake fasalin kudin Naira.
Ya ce dalilan da CBN suka ba shi sun tabbatar masa da cewa tattalin arzikin kasar zai amfana da raguwar hauhawar farashin kayayyaki, yawaitar jabun kudaden da ake yaɗa wa a kasuwannin duniya.
Buhari ya ce bai dauki wa’adin watanni uku na sauya sabbin takardun ba a matsayin sun yi kaɗan ba.
“Mutanen da ke da kudaden haram da aka binne a cikin ƙasa za su fuskanci kalubale da wannan amma ma’aikata, kasuwancin da ke da kudaden shiga ba za su fuskanci matsala ba,” in ji shugaban.
Shehu ya bayyana cewa, shugaban ya kuma yi magana kan batutuwan da suka shafi samar da abinci da tsaron kasa, da dai sauransu a cikin hirar.