Home Labarai Ƴan ta’adda sun saki ɗan takarar majalisa bayan biyan Naira Miliyan 3 kuɗin fansa

Ƴan ta’adda sun saki ɗan takarar majalisa bayan biyan Naira Miliyan 3 kuɗin fansa

0
Ƴan ta’adda sun saki ɗan takarar majalisa bayan biyan Naira Miliyan 3 kuɗin fansa

 

Ɗan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar PDP a mazabar Obi, Moses Egbodo, ya shaƙi iskar ƴanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi, bayan an biya Naira miliyan uku a ranar Asabar.

Daily Trust ta rawaito cewa Egbodo ya kwashe kwanaki shida a hannun masu garkuwa da mutane.

An yi garkuwa da shi ne tare da wasu mutane uku a cikin wata motar haya yayin da su ke tafiya daga Makurdi zuwa Otukpo a ranar Litinin da ta gabata.

Shugaban karamar hukumar Obi, Tony Akpa, wanda ya tabbatar da sakin sa ga manema labarai a Makurdi a jiya Lahadi ya ce, “An sako mutumin jiya (Asabar) da misalin karfe 7 na dare bayan ya shafe kwanaki shida a wani rami na masu garkuwa da mutane.

“An yi garkuwa da shi a ranar Litinin da ta gabata tare da wasu mutane uku yayin da suka fito daga Makurdi zuwa Otukpo. Ya shiga wata motar haya ne shine aka tare su akai awon-gaba da su.

“Da farko sun bukaci miliyan 4 a matsayin kudin fansa amma sun gama karbi miliyan 3.”

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Benue, SP Catherine Anene, ta ce ba ta da masaniya kan lamarin.