
Gwamna Babagana Zulum na Borno ya sanar da bayar da tallafin karatu na Naira miliyan 300 ga marayu 300 da suka rasu na ƴan ƙungiyar tsaro na sa-kai da su ke yaki da ta’addanci su ke tallafa wa sojoji.
Masu aikin sa-kai sun hada da jami’an rundunar hadin gwiwa ta farar hula, mafarauta da ƴan banga.
Da ya ke jawabi a wajen bikin a jiya Talata a Maiduguri, Zulum ya kuma bayyana karin kudaden alawus-alawus na ƴan agaji na wata-wata daga Naira 20,000 zuwa N30,000 da kuma alkawarin ba su kari na karshen shekara.
Zulum ya ce shigar da ƴan sa-kai wajen yaƙi da ƴan tada kayar baya ya yi nisa wajen samun nasara da za su taimaka wajen yaki da ƴan tada kayar bayan saboda sanin yankunan da suke ta’addancin.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta yi watsi da iyalan wadanda su ka sadaukar da rayuwarsu wajen samar da zaman lafiya ba, inda ya ce wannan shi ne kashi na farko na shirin da za a ci gaba da tabbatar da cewa an yi wa marayu duka.
Gwamnan ya kuma bayyana tallafin kudi, abinci da tufafi ga iyalan marayun, sannan ya yabawa sojoji da sauran kungiyoyin tsaro bisa hadin kai da suka yi wanda ya haifar da ingantaccen tsaro a jihar.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin bayar da tallafin karatu, Kaka-Shehu Lawan ya ce ta tantance tare da amincewa da mata 110 da maza 190.