Home Siyasa Aisha Binani ta ajiye muƙaminta na kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu

Aisha Binani ta ajiye muƙaminta na kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu

0
Aisha Binani ta ajiye muƙaminta na kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu
Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, Aishatu Dahiru Binani, ta yi murabus daga mukaminta na kodinetan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na jihar Adamawa.
MBinani, a wata sanarwa da ta sanya wa hannu da kan ta, ta ce ta ajiye mukamin ne har sai an kammala karar da ta shigar na cire ta a matsayin ƴar takarar gwamna ta jam’iyyar APC a jihar Adamawa.
A tuna cewa a ranar 14 ga Oktoba, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Yola ta soke zaben fidda-gwani na gwamna a Jihar, wanda Binani ta lashe.
“Sanata Aishatu Binani ta ajiye muƙaminta a matsayin kodinetan yakin neman zaben Tinubu/Shettima na jihar Adamawa har sai sakamakon karar da kotun daukaka kara da ta shigar ya fito.
Sanarwar ta kara da cewa “Na bukaci PCC da ta nada kodineta na wucin+gadi a halin yanzu.”
Murabus din nata na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kwamitin zartarwa na jihar, SEC, na jam’iyyar APC ta Adamawa, ya ki amincewa da kafa kwamitin yakin neman zaben da Sanatan ta kafa.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Samaila Tadawus, ya zargi Binani da naɗa mambobin kwamitin yakin neman zaben jihar da yin gaban kanta ba tare da tuntuɓar shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki ba.