
Shugaban Masu Rinjaye na Jam’iyyar APC a Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, mai wakiltar Doguwa/Tudunwada ya ce tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ba ƙashin yarwa ba ne.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Doguwa ya faɗa cikin rikici a jam’iyyar tun a makon da ya gabata, inda a ke zargin sa da jifan mataimakin ɗan takarar gwamna na APC, Murtala Sule Garo da kofin shayi, har ta kai ga ya ji masa rauni.
Sai dai kuma tuni Doguwa ya musanta wannan zargi, inda ya ce sun dai yi sa-in-sa har ta kai ga Murtala din ya yi yunkurin cin kwalar rigarsa (Doguwa), kuma a nan ne ya zame ya faɗi a kan kofin shayi, shi ne ya samu rauni.
Tun daga nan dai wutar rikicin ke ci gaba da ruwa a tsakanin Daguwa da Garo ɗin.
Da ya ke jawabi a wajen wani taro da ya yi da magoya bayansa a gidansa da ke Kano ran Juma’a, Doguwa ya ce Kwankwaso shugaba ne kuma ya bada gagarumar gudunmawa wajen ci gaban Kano.
A cewar Doguwa, rikicin sa da Kwankwaso ba na siyasa ba ne, illa kawai ɗan takarar shugabancin ƙasa na NNPP ɗin ya ƙi yi masa gaisuwa lokacin da mahaifin Doguwa ɗin ya rasu.
“Wallahi ko an ƙi ko an so Kwankwaso ba ƙashin yarwa ba ne. Kwankwaso gogaggen ɗan siyasa ne kuma shugaba ne. Na faɗa ɗin, sai dai in a yanka ni.
“Ni rigima ta da Kwankwaso ba ta siyasa ba ce ta jini ce. Bai yi min gaisuwar mahaifi na, Alhaji Ado ba. Tun da ko bai ga darajar mahaifi na ba, to ba ruwa na da shi; ai uba bai fi uba ba.
“Amma a yau idan Kwankwaso ya kira ni a waya, ko ya aiko da wakilci yai min gaisuwar rasuwar mahaifi na, to wallahi ba zan sake zagin sa ba. Ai siyasa ba gaba ba ce.
“Ni ba ɗan Kwankwasiyya ba ne ba kuma zan shiga Kwankwasiyya ba, amma dole a faɗi gaskiya cewa Kwankwaso shugaba ne, in ji Doguwa.