
Tsohon dan wasan kwallon kafar Ivory Coast da Chelsea, Didier Drogba ya ƙaryata labarin da ke cewa ya musulunta.
A jiya Litinin ne dai raɗe-raɗin cewa Drogba ɗin, wanda ya kuma taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Marseille ya karade kafafen sada zumunta.
Hakan ya faru ne bayan da wani malami ya wallafa hotonsa tare da tsohon dan kwallon suna addu’a a shafinsa na Twitter.
Malamin ya wallafa hoton, tare da cewa tsohon dan kwallon ya musulunta.
Sai dai kuma a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Drogba ya ce ba musulunta ya yi ba, addu’a kawai ya ke yi wa musulman kauyensu bayan da ya ziyarci kauyen nasu.
Ya bayyana cewa lokaci ne na nuna ”’yan uwantaka”
Daga baya malamin mai suna Mohamed Salah ya goge sakon da ya wallafa din, inda ya ce Drogba ba musulunta ya yi ba, to amma kuma zai ci gaba da yi masa addu’ar musulunta.