
Tiffany, ɗiyar tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, na shirin auren saurayinta Michael Boulos, wanda ya girma a Legas, Nijeriya.
A cewar wata mujalla mai suna Page Six, za a daura auren ne a ranar 12 ga watan Nuwamba, a wani wurin shakatawa na Mar-a-Lago, mallakin Trump da ke Florida.
Mujallar ta ce makusantan ma’auratan sun ce a na tsammanin baƙi sama da 500 ne za su halarci wajen bikin.
Boulos , wanda dan asalin kasar Labanon ne da kuma Faransa ya tashi ne a birnin Lagos na Nijeriya, inda mahaifinsa, Massad ke da kamfanin Boulos Enterprises kuma shine shugaban kamfanin SCOA Nigeria.