Home Labarai Sai da mu ka sayar da duk kadarorinmu sannan aka saki ƴaƴanmu, in ji matar tsohon AG na Zamfara

Sai da mu ka sayar da duk kadarorinmu sannan aka saki ƴaƴanmu, in ji matar tsohon AG na Zamfara

0
Sai da mu ka sayar da duk kadarorinmu sannan aka saki ƴaƴanmu, in ji matar tsohon AG na Zamfara
Matar tsohon akanta-janar na jihar Zamfara, Abubakar Furfuri, ta ce sai da su ka sayar da duk kadarorinsu sannan su ka biya kudin fansar da aka biya domin a sako ƴaƴansu mata guda biyar.
An sako ‘yan matan ne a ranar Litinin bayan da aka bayar da rahoton cewa iyalan sun biya maƙudan kuɗin fansa ga ƴan ta’addar.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an sace ‘yan matan ne daga gidansu da ke unguwar Furfuri a Ƙaramar Hukumar Bungudu ta jihar a cikin watan Maris.
Da take zanta wa da BBC Hausa kan halin da ta shiga cikin watanni bakwai da aka yi garkuwa da ƴaƴanta mata, mahaifiyar, wadda aka sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa iyalan sun biya kuɗin fansa ga ƴan ta’addan.
Ta ce an biya kudin fansa ne bayan da ita da mijinta suka sayar da kadarorinsu da kuma tallafin da ga ƴan uwansu.
Yayin da ta ke nuna godiya ga Allah da ya sa ‘ya’yan na ta su ka  fito daga hannun ƴan ta’addan lafiya, mahaifiyar ta bayyana cewa ‘ya’yan na ta mata sun tabbatar mata da cewa wadanda suka sace su ba su yi musu fyaɗe ba.
“Na yi matukar farin ciki da godiya ga Allah da ya dawo da su lafiya, duk da cewa sun gaya min yadda suka yi fama da cizon sauro da kuma zama a wani wuri mara daɗi.
“Abin farin ciki na shi ne sun tabbatar min da cewa ba a taɓa matancinsu ba iya tsawon watannin da su ka yi,” in ji ta.
Da take ba da labarin yadda ta ji bayan dan ta’addar ya fitar da wani faifan bidiyo a watan Oktoba yana barazanar kashe ‘ya’yanta idan har ba a biya su cikakken kudin fansa ba, ta ce, “Na firgita da takaici, amma na ci gaba da addu’a ga Allah da ya dube cikin wannan mawuyacin hali. Ban taba yanke fatan dawowar su ba, kuma Alhamdulilah abin ya faru.
“’Yan matan sun shaida min cewa ‘yan ta’addan a kullum suna yi musu barazana cewa ba za su bar dajin ba, sai dai idan iyayensu sun biya cikakken kudin fansa kamar yadda suka bukata, kuma babu wanda ya ba mu ko sisin kwabo, ni da mijina ne mu ka sayar da kadarorinmu masu daraja domin mu samu nasarar ceto rayuwarsu,” in ji mahaifiyar.