
An lakaɗa wa wani direban haya dukan kawo-wuƙa a Legas, mai suna Samson Adewunmi, har ta kai ga ya shiga halin rai-kokai-mutu-kokai a kan ya ƙi bada cuwa-cuwar Naira 500 a tashar mota.
Lamarin, a cewar jaridar Punch, ya faru ne a ranar Talata bayan da wasu da ake zargin ƴan tasha ne suka yi masa duka saboda ya ki biyan harajin N500 da ba na ka’ida ba .
Jaridar ta kuma tattaro cewa bas din Adewunmi, kirar Mazda, ita ma ta sha rotse a tashar motar Volks da ke kan hanyar Legas zuwa Badagry.
An ce Samson yana kan hanyarsa ta zuwa Mile 2 ne da misalin karfe 7 na safe, inda wasu ƴan gada-gada suka tare shi don neman ya basu N500.
Bayan ya ki biyan kudin, an ce sai su ka kai masa hari da sanduna da adduna, sannan su ka farfasa gilashin motar sa ta Mazda.
Samson ya samu rauni sosai, inda aka garzaya da shi wani asibiti da ke kusa, inda a halin yanzu yake cikin mawuyacin hali.
Abiodun Akintade, shugaban kungiyar jin dadin direbobi ta kasa JDWAN, wanda ya bayyana hakan a jiya, ya ce: “A ranar Talata, daya daga cikin mambobinmu direban motar Mazda mai suna Samson Adewunmi, an kai masa hari a tashar motar Volks ta jihar Legas, a kan hanyarsa ta zuwa Mile 2, da misalin karfe 7 na safe, akan kudi N500.
“An farfasa masa gilashin mota, kuma an yi masa dukan tsiya da adda, wanda hakan ya sa ya samu muggan raunuka a halin yanzu yana cikin suma a asibiti kuma muna fatan dai Allah Ya bashi lafiya,” in ji shi.