
Rundunar ƴan sanda ta ƙasa a jihar Borno, a jiya Laraba ta karyata rade-radin da ake yaɗa wa cewa an kai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar hari a wajen taro a Maiduguri.
Kakakin kwamitin kamfen din Atiku, Dino Melaye, a cikin wata sanarwa, ya ce akalla mutane 74 ne ke kwance a asibiti yayin da aka lalata motoci da dama lokacin da wasu ƴan daba suka kai hari kan ayarin motocin Abubakar a Maiduguri.
Sai dai kuma Kakakin rundunar ƴan sandan, ASP Kamilu Shatambaya, ya shaida wa manema labarai cewa, wannan zargi ba shi da tushe balle makama kuma ba shi da kanshin gaskiya a ciki.
Shatambay ya bayyana rahoton cewa an kai wa Abubakar hari ne a lokacin da yake jawabi a wani taro a Maiduguri, inda ya ce karya ne kwata-kwata labarin.
Ya bayyana labarin a matsayin na karya, yaudara da kuma yunkurin wasu marasa don zaman lafiya na tayar da tarzoma da kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.
Ya bayyana cewa an gudanar da taron cikin nasara a karkashin tsauraran matakan tsaro.