Home Ƙasashen waje Taliban ta hana mata zuwa wuraren shaƙata wa da wasanni

Taliban ta hana mata zuwa wuraren shaƙata wa da wasanni

0
Taliban ta hana mata zuwa wuraren shaƙata wa da wasanni

Ƙungiyar Taliban ta haramta wa mata zuwa wuraren shan iska da wasanni a babban birnin ƙasar Kabul, lamarin da ya zama sake ware mata daga duk wata cuɗanya da mutane a Afghanistan.

Wani mai magana da Ma’aikatar Kula da Ɗa’a ya shaida wa BBC cewa an gaya wa masu kula da wuraren shaƙatawa cewa kar su sake barin mata shiga.

Ƙungiyar ta ce ba a bin dokokin Musulunci a wuraren shaƙatawar.

Tun bayan da ƙungiyar ta ƙwace iko da ƙasar a watan Agustan 2021 aka sake tsaurara matakai kan ƴanci da walwalar mata.

A ƙarƙashin mulkin Taliban na nuna wariya ga wani jinsi, an bai wa mata izinin zuwa wuraren shaƙatawa ne kawai sau uku a sati – daga Lahadi da Litinin sai Talata -su kuma mata sau huɗu a mako.

A yanzu kuwa ba za a yarda mata su shiga wajen ba ko da ƙarƙashin rakiyar muharramansu maza.

“Mun yi hakan ne saboda cikin wata 15 da suka wauce ɗin nan duk da ƙoƙarinmu, to mutane ba sa bin dokokin Shari’ar Musulunci a ƙasar,” in ji Mohammed Akif, mai magana da Ma’aikatar Kula da Ɗa’a, kamar yadda ya cewa BBC.

“Wannan mataki ya shafi dukkan mata ne, ko sun je su kaɗai ko tare da muharrami.”

Haramcin ya haɗa har da wuraren wasanni da ake hawa ƙananan motoci da iyalai ke zuwa da yara.

Zuwa yanzu dai kamar dokar a babban birnin kawai ta fara aiki, amma a baya irin waɗannan dokoki sun shafi baki ɗayan sassan ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na reuters ya ga lokacin da wata mata ta je shiga waje wasannin amma sai aka hana ta.

Masooma wacce ba ta yarda an bayyana cikakken sunanta ba ta ce: “KAmata ya yi idan uwa ta je wajen da ƴaƴanta to a bar su su shiga, saboda yaran nan ba su ga wani abu mai kyau ba… don haka suna buƙatar su yi nishaɗi da