
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da asibitin bangaren shugaban kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Wanda aka gina tare da samar da kayan aiki a kan kudi naira biliyan 21, ya kasance wani gagarumin aiki abin koyi a gwamnatin Buhari.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha, ya kaddamar da sabbin ayyuka guda hudu a asibitin a jiya Alhamis.
Ayyukan sun haɗa da ɗakin gwaje-gwaje na Molecular Level 2, wanda Cibiyar Kula da Cututtuka ta Ƙasa, NCDC ta sahale, da kuma wani matsakaicin ɗakin ƙone cututtuka wanda ofishin kula da yanayin muhalli, ƙarƙashin ofishin SGF ya bayar.
Ginin faɗaɗa ɓangaren hakori da kuma ɗakunan ma’aikata me sashe biyu na asibitin da SGF ɗin shima ya kaddamar.
A jawabinsa a wajen taron, Mustapha ya bayyana ayyukan a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Buhari na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga ƴan Nijeriya.