
Wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu Kabiru ya saya wa al’ummar Karamar Hukumar Bichi dake Jihar Kano motocin ɗaukar gawa guda uku da babura guda biyar.
Kabiru, wanda a ka fi sani da Sabon-shafi, ya bada ababen hawan ne ga wasu kauyuka da su ke wahalar samun motar kai gawa a Bichi.
Da ya ke jawabi a wajen miƙa mukullayen motocin ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Sabon-shafi ya ce ya bada sadakar motocin ne sabo da wata rana ya ga an dauko gawa a kan babur mai ƙafa uku.
A cewar sa, yana tafiya sai ya ga an dauko gawar a babur mai ƙafa uku har kafafun mamacin na fito wa waje a kan hanyar su ta zuwa binne gawar.
“Wannan dalili ne ya sa na ci alwashin sai na kawo karshen karancin motar kai gawa a wasu sassa na Bichi,” in ji shi.
Ya ce baburan kuma guda 5 ya bada su ne kyauta ga ma’aikatan makabarta domin su rage wahalar zuwa wajen aikin nasu na hakar kabari.
A jawabin Hakimin Bichi, Alhaji Abdulhamid Bayero, yayin gabatar da Alhaji Jamilu Sabon-shafi a gaban sarki, a madadin Sarkin, ya yaba masa a bisa wannan kokari da yayi tare da yi masa addu’ar fatan alkhairi.