
Ƴan sanda a jihar Kebbi sun yi holon wani Bashiru Sani, dan kauyen Helende da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a gaban manema labarai a jiya Juma’a bisa zarginsa da mallakar takardun jabun kuɗi har na Naira 316,000.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora ne ya shaida wa manema labarai a Birnin Kebbi cewa, kudin ƴan Naira dubu-dubu ne.
“A yayin da ake gudanar da bincike, an kama babban wanda ake zargin, Samaila Umar (25) daga karamar hukumar Argungu, wanda ya buga kudin jabun ta hanyar na’ura mai kwakwalwa,” in ji shi.
Kontagora ya ce za a gurfanar da mutumin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Babban Bankin Ƙasa, CBN, ya sanar da canja fasalin takarar Naira a watan Disamba, inda za s canja fasalin naira 500, 200 da kuma 100.
Tun da ga lokacin sanarwar, Hukumar. Yaki da Cin-hanci da Rashawa, EFCC ta dukufa ta ke kama waɗanda su ke totse takardun kuɗaɗe da kuma masu canjin kuɗaɗen waje ba bisa ka’ida ba.