Home Siyasa An dakatar da shugaban jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a Zamfara

An dakatar da shugaban jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a Zamfara

0
An dakatar da shugaban jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a Zamfara

Jam’iyyar APC, reshen jihar Zamfara ta dakatar da shugaban jam’iyyar na Ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar, Shehu Buda Nasarawa, bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa.

Shugabannin jam’iyyar a jihar sun kuma amince da naɗin Tafa Nasarawa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na riko a karamar hukumar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar a Gusau a jiya Asabar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “wannan sanarwa ce ga jama’a cewa an dakatar da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Bukkuyum, Shehu-Buda Nasarawa.

“Kwamitin zartaswar jam’iyyar na jiha karkashin jagorancin Alhaji Tukur Danfulani ya amince da nadin Alhaji Tafa Nasarawa a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na yankin.

“Nadin ya fara aiki nan take, kuma an umurci tsohon shugaban da ya mika duk kayayyakin aiki na jam’iyya da ke hannunsa zuwa ga shugaban riko har sai an kammala bincike a kansa,”