Home Labarai Ƴan bindiga sun yi garkuwa da malami a Kwara, sun kuma buƙaci kuɗin fansa N100m

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da malami a Kwara, sun kuma buƙaci kuɗin fansa N100m

0
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da malami a Kwara, sun kuma buƙaci kuɗin fansa N100m

 

A ranar Asabar ne wasu ƴan bindiga suka yi awon-gaba da wani malami mai suna Sofiu Amolegbe da ɗansa Aliyu, a Oko-Olowo da ke yankin Ilorin a jihar Kwara.

Ƴan bindigar, wadanda suka kutsa kai gidan malamin domin aikata laifin, sun harbi wani ɗan uwanss mai suna Fasasi.

Jairdar Punch ta rawaito cewa da ya ke ba da labarin lamarin, mahaifin malamin ya ce masu garkuwa da mutanen da suke tunanin Fasasi ya mutu, sun yi wa dansa da jikansa bulala bayan sun kai su wani wuri da ba a bayyana ba.

Ya ce bayan da masu garkuwa da mutanen sun tafi, an garzaya da Fasasi wani asibiti da ba a bayyana ba inda yake jinya.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa Naira miliyan 100m domin su sako wadanda su ka sace.

Ya ce, “Masu garkuwa da mutanen sun tuntube mu kuma suna neman kudin fansa N100m. Mun roke su da su karbi N10m daga gare mu duk da cewa ba mu da kudin.

“Ina kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su taimaka mana wajen fitar da ‘ya’yana biyu daga hannun masu garkuwa da mutane,” in ji kakan.

Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Okasanmi Ajayi, ya ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifin.