
Wasu ƴan fashin jeji sun yi garkuwa da mutane hudu a kauyen Kolo da ke Ƙaramar Hukumar Gusau a jihar Zamfara.
A wani rahoto da gidan Talabijin na Channels ya fitar, a baya ƴan ta’addan sun bukaci Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa, amma bayan an yi ciniki, sun amince da karɓar Naira miliyan biyar.
Wasu majiyoyi a yankin sun kuma ce a yayin da mutanen kauyen ke kokarin haɗa kuɗin fansar ta hanyar haɗin gwiwa, masu garkuwa da mutanen sun aike da sako a ranar Talata cewa ba za su saki wadanda aka yi garkuwa da su ba har sai babban bankin Najeriya ya fitar da sabbin takardun kudi na Naira.
“A yayin da mu ke kokarin tattara kudaden da ‘yan ta’addan su ka nema, sai suka sake aikewa da wani sako cewa ba za su karbi tsofaffin takardun naira ba,” inji majiyar.
“Sun ce za su ci gaba da ajiye mutanen da aka sace a sansanonin su har zuwa wata mai zuwa – Disamba – lokacin da sabbin takardun Naira za su fara aiki.”
Kokarin jin martanin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ya ci tura.