Home Kasuwanci An ƙara farashin ‘pure water’ a faɗin Nijeriya

An ƙara farashin ‘pure water’ a faɗin Nijeriya

0
An ƙara farashin ‘pure water’ a faɗin Nijeriya

Kungiyar masu samar da ruwan leda, ATWAP, ta sanar da ƙarin farashin ruwan leda, wanda a ka fi sani da pure water daga Naira 200 zuwa N300 kan kowace leda ɗaya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugabar kungiyar ta kasa, Mrs Clementina Ativie ta fitar a Abuja.

Shugabar ta ce an cimma matsayar ne baki daya a yayin babban taron kungiyar ATWAP da aka gudanar a Abuja a jiya Laraba.

Clementina ta ce an samu canjin farashin ne sakamakon karin farashin kayan masarufi, hade da yanayin tattalin arzikin kasar.