
Ƙungiyar Ƙwallon Kafa ta Lobi Star da ke jihar Benue ta musanta rahotannin da ke cewa ta na zawarcin sharararren ɗan wasan nan, Cristiano Ronaldo, bayan ya raba gari da Manchester United.
A halin yanzu dai Ronaldo, wanda ke jan ragamar kasarsa Portugal a gasar Cin Kofin Duniya a Qatar, bashi da kungiya bayan Man United ta yanke kwantaraginsa.
Hakan ya faru ne bayan da Ronaldo ɗin ya yi wata hira da wani dan jarida, Piers Morgan, inda ya caccaki kungiyar, ya kuma ce ba ya ganin girman kocin ta, Erik Ten Hag.
Sai dai kuma bayan raba garin da Ronaldo ta yi da Man United, ana ta kawo raɗe-raɗin cewa kungiyoyi da dama na zawarcin sa, ciki har da Lobi Star.
Sai dai kuma tuni mahukunta a kungiyar su ka musanta wannan rahoto, inda su ka ce “babu wata magana da mu ka yi da Ronaldo ma cewa mu na son sayen sa”
A shafin ta na Twitter, Lobi Star ta ce a halin yanzu dai babu wata tattaunawa da ta ke yi da Ronaldo ɗin, wanda ya lashe gasar zakaran ƴan ƙwallon ƙafa ta duniya sau biyar rigis.
Amma kuma Lobi Star din ta ƙara da cewa “har yanzu ba mu tattauna da wakilan Ronaldo ba. Mu na masa fatan alheri.”