
Fursunoni 21 da ke zaman gidan yari daban-daban a Jos ne ke zana jarrabawar kammala karatun sakandare, SSCE, ta watan Nuwamba/Disamba 2022.
ASC Geofrey Longdiem, jami’in hulda da jama’a na Hukumar Gidajen Yari ta Ƙasa, reshen jihar Plateau ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a Jos.
A cewar Longdiem, fursunonin 21 da ke zana jarabawar, wanda hukumar jarrabawar NECO ta shirya a cikin gidan gyaran hali, sun kunshi maza 15 da mata shida.
Ya bayyana cewa matakin na daya daga cikin aikin hukumar da aka tsara na samar wa fursunoni rayuwa mai amfani ga kansu da iyalai da kuma al’umma bayan kammala zaman gidan yari.