Home Siyasa Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

0
Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar wa al’ummar Najeriya cewa, ba a ajiye na’urorin tantance masu kada kuri’a (BVAS) a wuraren da ƴan bangar siyasa su ka kai hari tare da kona su kwanan nan ba.

INEC ta kuma ce wasu muhimman kayyakin da za a yi amfani da su wajen gudanar da zabukan 2023 su na nan lafiya ƙalau cikin tsaro.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri’a, Mista Festus Okoye ne ya sanar da hakan a wani shiri na gidan Talabijin na Channels a jiya Lahadi.

Okoye ya sake nanata cewa za a gudanar da babban zaben kasar na shekara mai zuwa duk da hare-haren da aka kai wa ofisoshinta.

Hukumar zaben kasar ta koka kan yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa, inda adadin ofisoshin da abin ya shafa ya kai 50, a fadin jihohi 21.

Sai dai yayin da yake magana a jiya, Okoye, ya ce muhimman kayan da za a tura domin zaben badi ba sa cikin wuraren da aka kai harin kwanan nan.

“Ina so in tabbatar wa al’umma cewa kayanmu masu mahimmanci ba sa cikin wadannan wuraren da wadannan hare-haren suka faru.

“Mun tabbatar da tsaron tantance masu kada kuri’a (BVAS) da sauran wasu muhimman abubuwa da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaben.

” Wadannan kayan ba sa cikin wadannan wuraren da ake kai wa hari,” in ji Okoye