Home Labarai Ƴan garuwa sun tafi yajin aiki bisa dukan ɗan uwansu a Kano

Ƴan garuwa sun tafi yajin aiki bisa dukan ɗan uwansu a Kano

0
Ƴan garuwa sun tafi yajin aiki bisa dukan ɗan uwansu a Kano

Al’ummar unguwar Hotoro Danmarke a jihar Kano sun fada matsalar ruwa sakamakon rufe sayar da ruwa da ƴan garuwa su ka yi a yankin da kewayensa.

Masu sayar da ruwan sun yanke shawarar ne bayan da wasu mazauna yankin su ka daki wani ɗan garuwa sabo da ya ƙi sayar musu da ruwa.

Wani mai sayar da ruwa, Malam Yahuza Lawan, wanda ya shaida lamarin ya ce sun yanke shawarar daukar matakin ne saboda wasu mazauna yankin sun lakaɗa wa ɗan uwansu dukan tsiya.

A cewar Lawan, wani mazaunin unguwar ne garin ya bukaci ɗan garuwa da aka daka da ya sayar masa da ruwa, inda shi kuma ya ce wani ya riga ya saye kurar, sai dai idan ya dawo sai ya kai masa.

Ya kara da cewa a lokacin da ya ki bin su saboda yana kan hanyarsa ta kai ruwa ga wani kwastoma da ya riga ya biya kuɗinsa, sai su ka fara lakada masa duka har suka raunata masa ido daya.

Lawan ya kuma yi zargin cewa mazauna yankin sun yi sanadiyyar mai sayar da ruwan ya rasa idonsa.

“Yanzu haka yana asibiti ana jinyarsa. Likitocin sun shaida mana cewa ya rasa idonsa sakamakon mummunan dukan da aka yi masa.

“Saboda haka, mun yanke shawarar dakatar da sayar da ruwa a yankin, kuma tuni wasu daga cikinmu sun riga sun yi tafiyarsu gida yayin da waɗanda ke nan suka ƙi ci gaba da sayar da ruwa.

“Dole ne mu ɗauki wannan matakin kan abin da ya faru da dan uwanmu. Membobinmu sun sha fama da cin zarafi, don haka ba za mu sake lamuntar hakan ba,” in ji Lawan.

Shi ma Adamu Khalil mai sayar da ruwa ya nuna ɓacin ransa, inda ya ce ya rufe wurin sayar da ruwan don mara wa ƴan garuwar yankin baya.

“Sun yi masa dukan tsiya ne saboda ya ki sayar musu da ruwa bayan da ya ce su jira shi ya kai ruwan ga wani kwastomansa wanda tuni ya biya kudinsa.

“Mun dakatar da sayar da ruwa har sai an yi abin da ya dace. Mun ji cewa jami’an ‘yan sanda reshen Hotoro sun cafke babban wanda ake zargin. Mu na so a yiwa dan uwanmu adalci.” Inji Khalil.

Matakin na ƴan garuwar ya haifar da karancin ruwan sha a yankunan Danmarke, Hotoro Bayan Depot, Unguwa Uku Kauyen Alu da dai sauransu.

Tuni mazauna yankin su ka fara gani tasirin boren na ƴan garuwar.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce zai bincika lamarin.