
Dakaru na musamman na Rundunar Sojin Ƙasa da sauran dakaru sun sake samun nasarar fatattakar ‘yan bindiga, inda har su ka hallaka 9 a wani kazamin fada da aka gwabza a wasu wurare a Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis a Kaduna.
Aruwan ya ce an bayyana hakan ne a wani rahoto da aka mika wa gwamnatin jihar na cewa sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan a sansanonin su a kogin Rafin Sarki tare da kashe biyar da ke kusa da wurin, yayin da wasu da dama suka tsere.
Ya kara da cewa, a wani kazamar arangamar da su ka yi, sojojin da dakarun na musamman sun fatattaki wata maboyar dajin Galadimawa, inda ‘yan bindiga hudu suka rasa ran su a fafatawar.
A cewarsa, ƴan bindigar sun gudu sun bar mata da kananan yara da su ka yi garkuwa da su, sai sojojin suka taho da su.
Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufa’i ya yaba da irin namijin kokarin da jami’ai da mutanen suka yi, sannan ya kara gode musu bisa irin nasarorin da suka samu da kuma nasarar ceto wadanda lamarin ya shafa.
Ya kara da cewa ana ci gaba da kai hare-hare a yankunan da aka gano a fadin jihar.
“Gwamnatin jihar a haka tana kira ga ‘yan kasa da su ci gaba da bayar da bayanan sa kai kan ‘yan fashi da maboyarsu da kuma masu ba da labari da kayan aiki, ta layukan waya: 09034000060, 08170189999,” Mista Aruwan ya ce.