Home Siyasa Kwankwaso ya ziyarci Ooni na Ife bayan buɗe ofishin jam’iyya

Kwankwaso ya ziyarci Ooni na Ife bayan buɗe ofishin jam’iyya

0
Kwankwaso ya ziyarci Ooni na Ife bayan buɗe ofishin jam’iyya

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya ziyarci Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

A ziyarar da ya kai wa Sarkin, Kwankwaso ya kaddamar da ofisoshin yakin neman zaben NNPP a Osun da makwabciyar ta, jihar Ekiti.

A wata sanarwa da ya fitar ta shafin sa na Twitter a jiya Asabar, dan takarar jam’iyyar ta NNPP ya yabawa ‘ya’yan jam’iyyarsa kan tiri-tiri da su ke yi da jam’iyyar.

Ya ce, “Na samu karramawa ta kaddamar da wasu ofisoshin @OfficialNNPPng a garuruwan Ile-Ife da Osogbo, jihar Osun. Ina yaba wa maza da mata na jam’iyyarmu bisa gagarumin aikin da suka nuna, kuma ina kara musu kwarin gwiwa da su kara himma.

“Na samu karramawa na kaddamar da wasu ofisoshin @OfficialNNPPng a garuruwan Ile-Ife da Osogbo, jihar Osun.

“Na kai ziyarar ban girma ga Ooni na Ife, Mai Martaba Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II, a fadarsa da ke Ile Ife, Jihar Osun.

“Muna matukar godiya ga Mai Martaba Sarki, Majalisar Ife, da kuma mutanen Ile Ife bisa gagarumin tarbar da suka yi mana,” in ji Kwankwaso.