
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya sha alwashin bada kashi 95 na kuri’un jihar Borno ga jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.
Ya ce ba zai taba cin amanar dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar, Kashim Shettima ba.
Mista Zulum ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin yakin neman zaben mata na jam’iyyar APC, karkashin jagorancin uwargidan dan takarar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, jiya Asabar a Maiduguri.
“Bani da wata mafita face in ga na tabbatar da nasarar takarar shugaban kasa ta Tinubu/Shettima da kuma jam’iyyar APC baki daya. Ba zan ci amanar Kashim Shettimaba,” ya sha alwashin.
Gwamnan ya tuno da yadda Mista Shettima ya nada shi shugaban makarantar Ramat Polytechnic, a lokacin da yake koyarwa a jami’ar Maiduguri, sannan kuma ya zama kwamishinan ma’aikatar sake gina gine-gine, gyara da sake tsugunar da jama’a, sannan kuma ya tabbatar da ya gaje shi a matsayin gwamnan jihar. .
“Za mu yi aiki tukuru don samar da kashi 95 na kuraun jihar Borno ga APC,” in ji Mista Zulum.
Har ila yau, da take jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zaben mata na yankin Arewa maso Gabas, uwargidan gwamnan, Falmata Zulum, ta bayyana Mista Shettima a matsayin wani abin arziki ga kasar nan, inda ta yi nuni da cewa, ya kafa hanyar samar da shugabanci nagari a jihar.
Ta ce, “APC ta yi wa mutanen Arewa maso Gabas komai ta hanyar ba mu mukamin mataimakin shugaban kasa.
“Na yi kira ga kowa da kowa, musamman mata, da su hada kai da Tinubu/Shettima da APC domin cimma wannan buri.”