
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta zargi wasu ‘yan siyasa da siyan katin zabe na dindindin (PVCs) da kuma baiwa masu zaɓe kudi don karɓar bayanan su na katin zaɓe wato VIN.
Kwamishina a INEC mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Nasarawa, Kaduna da Plateau, Mallam Mohammed Haruna ne ya bayyana haka a Abuja, yayin kaddamar da shirin #VoteMatters na kungiyar NESSACTION mai sa ido kan zabe a ranar Litinin.
Hukumar ta kuma ce a baya-bayan nan an yanke wa wasu mutane biyu hukunci bisa laifin mallakar katin zabe ba bisa ka’ida ba a jihohin Sokoto da Kano.
Gidauniyar International Foundation for Electoral System (IFES) ce ta tallafa wa shirin tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Ci Gaban Ƙasashen Duniya (USAID) da Ofishin Harkokin Waje, Commonwealth da kuma Ci gaba.
Haruna ya ce, “Muna sane da cewa wasu ‘yan siyasa na saye PVC. Idan ka karbi PVC din sannan ka sayar da shi ko ka bar wani ya mallaka, kana taimaka wa mallakar PVC ba bisa ka’ida ba wanda laifi ne a cikin dokar zabe.
“Wasu daga cikin ku na sane da cewa a baya-bayan nan ne INEC ta yi nasarar hukunta wasu mutane biyu da aka samu da laifin mallakar PVC ba bisa ka’ida ba a Kano da Sakkwato.
“Don haka ina kira ga jama’a da su tattala katinan su na PVC, su kiyaye su, sannan kuma a tabbatar da cewa ranar zabe za ku fita ku kada kuri’a, domin ko shakka babu ba za ku samu damar ƴancin ku na zaɓe.”