
Jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Katsina ta hana ta amfani da filin wasa na Muhammadu Dikko wajen taron ta na yaƙin neman zaɓen shugaban kasa.
Jam’iyyar ta tsara ranar Talata 20 ga watan 2022 domin gudanar da yakin neman zaben ta a jihar.
Dakta Mustapha Inuwa, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku-Lado ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Lahadi a Katsina.
Inuwa ya ce kwamitin ya rubuta wa gwamnatin jihar wasika sau biyu bisa neman ta izinin amfani da filin wasan.
Ya bayyana cewa, a amsar da gwamnatin jihar ta bayar kan wasiku biyu na jam’iyyar, ta ce har yanzu ana ci gaba da gyare-gyare a wurin, don haka ba za a iya amfani da su wajen taron ba.
Sai dai kuma Inuwa ya ce guraren da gwamnatin jihar ta yarje musu su yi taron sun yi cikin jama’a, ba za su dace da taron siyasa irin wannan ba.
Shima a nashi ɓangaren, Babban daraktan yakin neman zaben Atiku-Lado kuma shugaban kwamitin, Sen. Ibrahim Umar-Tsauri, ya nuna matukar damuwa kan martanin da gwamnatin jihar ta mayar.
Umar-Tsauri ya bayyana faruwar lamarin a matsayin abin bakin ciki da kuma kalubalen dimokuradiyya, yana mai cewa taron nasu ne na shugaban kasa, gwamna da sauran ‘yan takarar jam’iyyar PDP a jihar.