
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi alkawarin yin hijira idan ya mika mulki ga wanda zai gaje shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, domin kada ya tsoma baki cikin gwamnatin da ke tafe.
Gwamnan, wanda ya bayyana kwarin guiwar cewa Sanata Uba Sani ne zai gaje shi, ya ce ba zai yi wani katsalandan “a cikin tafiyar gwamnatin APC mai zuwa.”
Daily Trust ta rawaito cewa El-Rufai, wanda ya yi magana a wani taro na shiyyar Sanata ta tsakiya ta a jiya Litinin, ya ce ya san sanatan sama da shekaru 20 kuma Sani ya nuna bajintar sa a siyasance.
Ya shawarci al’ummar jihar Kaduna da kada su damu Uba Sani da bukatu na ba mukamai ko kwangiloli idan ya zama gwamna.
El Rufa’i ya bayyana Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya cancanta da zai kai jihar Kaduna matsayi mafi girma idan aka zabe shi a matsayin gwamna.
A nasa jawabin, Sani ya ce ya kasance dalibin “Malam Nasir El-Rufai a siyasa ” a cikin shekaru 20 da suka wuce kuma ya samu ‘digiri’ da dama a dalilin haka.
Sanatan wanda ya yi alkawarin ci gaba da tsare-tsare na gwamnatin El Rufa’i, ya yaba wa gwamnan kan sake farfado da harkokin mulki a jihar Kaduna.
Uba Sani ya ce gwamnati ba za ta iya daukar nauyin tallafin ilimi ita kadai ba, ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su dauki nauyin karatun boko amma marasa galihu zuwa manyan makarantu.
A cewarsa, a kwanakin baya ya baiwa dalibai 280 tallafin karatu a manyan makarantun jihar Kaduna domin su ci gaba da karatunsu.