Home Siyasa Rikicin takarar gwamna na PDP a Kano: Wali, Abacha da Bello za su san makomarsu ran Alhamis

Rikicin takarar gwamna na PDP a Kano: Wali, Abacha da Bello za su san makomarsu ran Alhamis

0
Rikicin takarar gwamna na PDP a Kano: Wali, Abacha da Bello za su san makomarsu ran Alhamis

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta sanya ranar Alhamis domin yanke hukunci a kan yakin neman tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar.

Daily Trust ta rawaito cewa ƴan takarar uku da suka haɗa da Mohammad Sani Abacha da Sadiq Aminu Wali da Jaafar Sani Bello na ta fafutukar ganin sun samu tikitin takarar jam’iyyar a Kano biyo bayan zabukan fidda-gwani da aka yi.

A zaman da aka yi na ci gaba da sauraron karar a jiya Litinin, an sanar wa da mutanen uku ta hannun lauyoyinsu cewa za a gabatar da hukuncin da aka shirya a ranar ta hanyar manhajar Zoom a ranar Alhamis.

Abacha, ta hanyar sammaci, ya je kotun, yana neman ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar a ranar 25 ga Mayu, 2022.

Ya kuma roki kotun da ta hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da jami’anta daga kara amincewa da Sadiq Aminu Wali ko wani mutum a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a Kano a zaben 2023.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da kuma buga sunan Sadiq Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar PDP biyo bayan mika sunan Wali da hedikwatar jam’iyyar ta kasa ta yi.

Sai dai a yayin da Abacha ke neman tikitin tsayawa takara a kotun, wani dan takara, Jafar Sani Bello ya shigar da sabuwar kara yana kalubalantar Mohammed Abacha da Sadiq Wali bisa zargin cancantar su kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar da dokar zabe da kuma kundin tsarin mulkin PDP.

Bayan haka ya samu izinin kotu ya shigar da kara a kan Wali da sauran masu kara.

Da ya ke nuna rashin gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke na ba Bello izinin shiga da shi a kara, Wali ya garzaya kotun daukaka kara yana neman ta soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

Don haka kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraren karar, saboda bai kamata a hada shi da Wali a cikin karar ba.

A lokacin da aka ci gaba da sauraren karar a babbar kotun tarayya a ranar 8 ga watan Disamba, 2022, alkalin kotun ya sanya ranar 19 ga watan Disamba domin yanke hukunci bisa hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.