Home Labarai Dalilin da ya sa na ci gaba da aiki da Ministan Abuja — Buhari

Dalilin da ya sa na ci gaba da aiki da Ministan Abuja — Buhari

0
Dalilin da ya sa na ci gaba da aiki da Ministan Abuja — Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello bisa nuna gaskiya da rikon amana a matsayin sa na ministan babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi jagorancin shugabancin babban birnin tarayya Abuja da wakilan al’umma, wadanda su ka kai masa gaisuwar Kirsimeti a fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja, a jiya Lahadi.

A cewar shugaban na Nijeriya, ya nada Bello a matsayin ministan babban birnin tarayya ne, kuma ya ki sauke shi saboda kyawawan halayensa.

Ya ce Bello ya nuna cewa shi ne mafi nagarta wajen kula da harkokin kudi da na al’umma a matsayin minista.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya ruwaito cewa, shugaban kasar na mayar da martani ne kan wata shaida da Smart Adeyemi, shugaban kwamitin majalisar dattijai a babban birnin tarayya Abuja, ya bayar, inda ya bayyana ministan na babban birnin tarayya Abuja a matsayin minista mafi gaskiya da rikon amana a tarihin babban birnin tarayya Abuja.

Buhari ya ce bai yi mamakin jin irin wadannan kalamai ma yabo kan Ministan Babban Birnin Tarayya ba, inda ya gode wa Bello da bai ba shi kunya ba.

Ya ce: “Ministan ya kawo canje-canje wajen harkar filaye a babban birnin tarayya Abuja. Ana amfani da mutane wajen sayar da filayen da ake yanka wa, maimakon gina su kamar yadda dokokin FCT suka tsara.

“Wasu kuma suna neman fili ne kawai don su sake siyarwa kuma su sami kuɗi cikin gaggawa don su samu kuɗi su ƙara aure.”

A kan bikin Kirsimeti, shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya bisa yadda suka amince da ba shi damar zama shugabansu.