Home Labarai An kama kwamandan IPOB wanda ya kashe Ahmed Gulak

An kama kwamandan IPOB wanda ya kashe Ahmed Gulak

0
An kama kwamandan IPOB wanda ya kashe Ahmed Gulak

Sojojin Nijeriya sun kama mataimakin kwamandan masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, wani Nwagwu Chiwendu wanda kuma ke da alhakin kashe wani dan siyasar Arewa, Ahmed Gulak.

PRNigeria ta jiyo cewa Chiwendushi ne babban mai horas da ƴan kungiyar ta IPOB kan sarrafa makamai, inda ya samu matsayin zama mataimaki ga shugaban ƙungiyar, Temple, wanda yanzu shi ne shugaban kungiyar a jihar Imo.

Shahararren mai laifin ya gudu daga aikin sojin Nijeriya, ya shiga ƙungiyar ta IPOB tun ranar 21 ga watan Janairu.

“Ya yi aiki a OPHK kuma don haka yana da kwarewar aiki. An kama shi ne a jiya yayin jana’izar mahaifinsa a Mbaise. Zai kai mu sansanin su a daren yau a Obowo.

“Ya amsa laifin kashe Gulak kuma ya tabbatar da cewa yaransa ne ke da alhakin yin garkuwa da wasu ‘yan kasashen waje guda 2 a kan hanyar Owerri-Okigwe da kuma kashe sufeto ‘yan sanda 2 da ke yi musu rakiya.

“Su ne kuma su ka kashe sojojinmu a wuri guda tare da kona mana Hilux a makon jiya. Haka kuma sun taka rawa a harin da aka kai ofishin INEC a Owerri.

“Yanzu haka yana tare da ‘yan sanda,” wata majiyar soja ta shaida wa PRNigeria.