Home Siyasa Maigida na ya dena kirana da ‘baby’ sai dai ‘Labour Party’, inji Aisha Yesufu

Maigida na ya dena kirana da ‘baby’ sai dai ‘Labour Party’, inji Aisha Yesufu

0
Maigida na ya dena kirana da ‘baby’ sai dai ‘Labour Party’,  inji Aisha Yesufu

Shahararriyar ƴar fafutukar nan, Aisha Yesufu, ta ‘koka’ da yadda ta rasa sunanta na soyayya da ga mijin ta a sakamakon harkokin siyasarta na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa, a cewar Aisha Yesufu, duk sunaye masu dadi da mai gidan ta, Aliu Osigwu Yesufu, ke kiranta da su, yanzu ya maye gurbinsu da ‘Labour Party’.

Sai dai kuma Aisha Yesufu ta ce ta ƙagu lokacin zaben 2023 ya zo ya wuce ba domin masoyin na ta ya ci gaba da kiran ta da duk sunaye masu daɗi da ya saba kiran ta da su.

“Mijina yanzu yana kira na da Labour Party maimakon ‘baby’ ko ‘Osotse’ (kyakkyawa) da yakan kira ni,” in ji ta.

“Na ƙagu a kammala zabe don in koma zama baby da na saba ji,” in ji Yesufu.