Home Labarai An harbe ɗan sanda a harabar banki, a ka kuma ɗauke bindigarsa a Bayelsa

An harbe ɗan sanda a harabar banki, a ka kuma ɗauke bindigarsa a Bayelsa

0
An harbe ɗan sanda a harabar banki, a ka kuma ɗauke bindigarsa a Bayelsa

Rahotanni na nuni da cewa an harbe wani ɗan sanda har lahira a harabar wani banki da ke kan titin DSP Alamieyeseigha a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Maharin ya kuma sace bindigar ɗan sandan.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare.

Rahotanni sun kara da cewa, wanda ake zargi da kisan, a makon da ya gabata, marigayin ya gabatar da shi ga jami’an bankin a matsayin dan uwansa wanda ya bayyana sunansa da David.

A cewar majiyoyin, wanda ake zargi da kisan ya kasance tare da marigayin a bankin inda ya ke gadi har tsawon mako ɗaya, inda a ka ce “Al’amarin ya faru ne a lokacin da su biyun ke cin abinci.

Yayin da dan sandan ya ajiye bindigarsa a kan benci ya na wanke cokalin da za su ci abincin, sai shi David ɗin ya dauki bindigar ya harbe shi a daf da daf,” inji wata majiya. Ta ce an garzaya da shi asibitin tarayya inda aka tabbatar da rasuwarsa washegari.

A cewar majiyar, tuni ‘yan sanda su ka fara gudanar da bincike kan lamarin tare da kokarin kwato bindigar da aka sace.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Asinim Butswat, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Butswat ya ruwaito cewa: “A ranar 29 ga Disamba, 2022, wani dan sanda, Cpl Bob, da ke bakin aiki a wani banki a Yenagoa ya mutu bayan da wani da su ke tare ya harbe shi a harsbsr bankin.

“An san ainihin wanda ake zargin kuma a bincike,”