Home Siyasa Sarkin Bauchi ya kori Wazirin Bauchi bisa rashin biyayya ga gwamna Bala Mohammed

Sarkin Bauchi ya kori Wazirin Bauchi bisa rashin biyayya ga gwamna Bala Mohammed

0
Sarkin Bauchi ya kori Wazirin Bauchi bisa rashin biyayya ga gwamna Bala Mohammed

Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu ya amince da tuɓe rawanin Bello Kirfi a matsayin Wazirin Bauchi kuma dan majalisar masarauta.

Kirfi, wani babban aminin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a siyasance yana takun saka da Gwamnan Bauchi sabo da nuna goyon baya ga Atikun a wajen babban taron jam’iyyar.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Janairu, mai dauke da sa hannun sakataren majalisar, Shehu Muhammad, majalisar masarautar Bauchi ta ce gwamnatin jihar ta bada umarnin tsige Kirfi saboda rashin biyayya ga gwamnan.

A takadar, mai lamba MLG/LG/S/72/T da kwanan wata 30 ga Disamba, 2022 ta ce, “abin da ke cikin wasikar ya nuna rashin biyayyar ka da rashin mutunta Gwamnan Jihar da gwamnati. Don haka ya ba da umarnin cire ka nan take.

“Saboda abubuwan da suka gabata, an cire ka daga mukamin Wazirin Bauchi da kuma ɗan majalisar masarautar Bauchi. Ina yi maka fatan alheri a duk abin da ka sa a gaba,” in ji wasiƙar.

A tuna cewa a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Nuwamba 3, 2022 da ya kuma aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyochia Ayu, gwamnan ya zargi tsohon Atiku da yin aiki tare da hadin gwiwar wasu masu goyon bayan “Bala Must go” a jihar domin yin zagon kasa a zaben da ya sake tsayawa takara a matsayin gwamnan jihar.

Majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa cewa ƴan rajin “Bala Must go” sun hada da Kirfi, tsohon gwamna Adamu Mu’azu da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.