
Sakataren karamar hukumar Sumaila a jihar Kano, Dalha Alfindi, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta NNPP.
Mafindi ya fice daga APC ne tare da ɗaukacin kansiloli 11 na Ƙaramar Hukumar a lokacin da ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu ya isa Kano domin gudanar da taron yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na shiyyar.
A wajen gangamin, Tinubu ya shaida wa ɗumbin jama’a a filin wasa na Sani Abacha cewa ya je Kano ne domin ya yi rawa domin jin daɗin tarbar da aka yi masa, inda ya nuna kwarin guiwar sa na samun nasarar lashe zaben shugaban kasa.
Sai dai a cikin wasikar murabus din da aka aike wa jaridar DAILY NIGERIAN a jiya Laraba, jami’an kananan hukumomin sun bayar da hujjar musgunawa ƴan jam’iyyar da shugaban karamar hukumar ke yi a matsayin dalilin murabus din nasu.
Majiya mai tushe ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa sakataren karamar hukumar da kansilolin da tun farko dan takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu a jam’iyyar NNPP, Kawu Sumaila ya mika sunayensu ga mukaman, sun yi murabus daga mukaminsu domin shiga yakin neman zabensu.
Kansilolin su ne Mustapha Haladu, mazaɓar Sumaila; Umar Umar, mazaɓar Sitti; Nuhu Ado, mazaɓar Gala-Gala; Abubakar Ahmed, mazaɓar Magama da; Ismail Salisu, mazaɓar Gani.
Sauran su ne Ibrahim Abubakar, Massu; Ma’amiru Nuhu, Rumo mazaɓar; Atiku Idris, mazaɓar Garfa; Umar Abdussalam, mazaɓar Kanawa; Sule Adamu, mazaɓar Rimi da; Danjuma Sale, mazaɓar Gediya.