
Masarautar Kazaure da ke Jihar Jigawa ta raba zakkar hatsi da dabbobi na sama da Naira miliyan 8.5 ga marasa galihu 220,012 a yankin.
Mai magana da yawun masarautar, Gambo Garba ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasar, NAN, a yai Asabar.
Malam Garba ya ce shugaban kwamitin tattarawa da rabon zakka na majalisar masarautar, Bala Muhammad ne ya bayyana hakan a taron raba zakkar a gundumar Amaryawa.
Ya kara da cewa an raba zakka mai kunshe da dabbobi da hatsi ga iyalai da suka cancanta a Yankewa Tuntube da ke gundumar Amaryawa a ranar 1 ga watan Janairu.
Kakakin ya kara da cewa, Muhammad ya danganta nasarar da kwamitin ya samu a yayin gudanar da atisayen da goyon baya da hadin kai da aka samu daga majalisar masarautar.
A cewarsa, Sarkin Kazaure, Najeeb Hussaini, ya yi kira ga masu hannu da shuni a yankin da su ci gaba da bayar da Zakka domin tallafa wa marasa galihu da masu karamin karfi a cikin al’umma domin rage radadin talauci.
Malam Garba ya kara da cewa, sarkin ya kuma bukaci iyaye da masu kula da yankin da su tabbatar da tarbiyyar ‘ya’yansu da tarbiyyar su yadda ya kamata.