Home Labarai Hukumar SSS ta musanta neman takardar izinin kama shugaban INEC na ƙasa

Hukumar SSS ta musanta neman takardar izinin kama shugaban INEC na ƙasa

0
Hukumar SSS ta musanta neman takardar izinin kama shugaban INEC na ƙasa

Hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta karyata rahoton da aka buga ta yanar gizo, inda aka ce ta nemi kotu ta yarje mata ta kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Mahmoud Yakubu.

Jami’in Hulda da Jama’a na SSS, Peter Afunanya, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, ya ce an ja hankalin hukumar ne kan wani rahoto da jaridar Daily Trust ta buga ta yanar gizo a ranar 5 ga watan Janairu, 2023 inda ta ruwaito cewa “Kotu ta dakatar da DSS daga kama shugaban INEC”.

A cewarsa, jaridar ta canja bayanan abin da ya faru a Kotun kuma ta ruwaito shi ba a mahallin sa ba.

Kakakin SSS din ya bayyana cewa, jaridar, duk da cewa ta ce abinda a ka buga s shafin ta na yanar gizo ya bambanta da na bugun takarda, sai kuma ta yi buris da alkawarin da ta ɗauka na fayyace gaskiyar lamarin.

“Wannan sanarwar, duk da haka, na da
mahimmanci domin fahimtar da al’umma, musamman ma da ya ke rahoton ba gaskiya ba ne.

“Rahoton ya nuna cewa hukumar mu ce ta ke kotu don neman izinin ta kama Shugaban INEC .

“Duk da haka, Ma’aikatar tana sane da yadda wasu miyagu ke son tada rikici a kasar nan, gami da haifar da cece-kuce game da babban zabe mai zuwa.

“Don haka hukumar SSS ta gargadi wadannan mutane da kungiyoyi da su dena irin wannan yaudara, inda ta shawarci duk masu ruwa da tsaki da su yi taka tsantsan tare da dakile yunkurin amfani da su wajen dakile dokar.