
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanya dokar hana fita daga garin Lambata da ke Ƙaramar Hukumar Gurara, sakamakon wani kazamin rikici da ya kai ga kashe Dagacin kauyen, Mohammed Abdulsafur.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Ahmed Matane ya fitar ranar Lahadi a Minna.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, wasu ɓatagari sun kashe hakimin kauyen na Lambata a ranar Asabar, a wani rikici da ya barke.
Hakan ne ya sanya Gwamna Bello ya bayar da umarnin sanya dokar hana fita a garin, da ga ƙarfe 6.00 na dare zuwa karfe 6.00 na safe, daga jiya Lahadi, har zuwa wani lokaci.
Ya ce, sanya dokar ta-ɓacin ya zama dole domin a taimaka wa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura, da ceton rayuka da kuma maido da doka da oda.
A cewar gwamnan, gwamnati ta yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da rashin bin doka da oda da suka faru a garin Lambata.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su ba jami’an tsaro hadin kai domin dawo da zaman lafiya a garin, ya kuma bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar hana fitar.