
A yau 16 ga watan Junairu, 2023 Babban Bankin Ƙasa, CBN, ya fara shirin kaddamar da katin cirar kuɗi na bai-ɗaya da ya ƙirƙiro da shi.
Daraktan Sashen Yaɗa Labarai na CBN, Osita Nwanisobi, ne ya sanar da hakan a karshen mako.
A cewarsa, an kera katin ne da hadin gwiwar hukumar kula da harkokin bankunan Najeriya, NIBBS, da nufin haɗe hada-hadar kuɗi a Najeriya da kuma shigo da al’ummar da ba su da asusun banki.
Ya yi nuni da cewa, ana sa ran katin zai yi gogayya da sauran katunan cirar kudi da suka hada da Mastercard, Discovery, da Visa card, inda ya ƙara da cewa amma a halin yanzu, katin ba zai iya aiwatar da hada-hadar kudaden kasashen waje ba.
Ya kara da cewa hakan ya samo asali ne daga saurin kirkiro fasahar zamani da da kara shigar da wayar hannu, da kuma tsare-tsare masu inganci na CBN wadanda suka haifar da daukar ayyukan hada-hadar kudi na zamani da ba a taba yin irinsu ba.”
Ya zayyana fa’idodin tsarin katin da su ka haɗa da rage farashi da amfani da kuɗin waje, da kare martabar bayanai, ba da damar shawarwarin da suka dace a cikin gida, da kuma sanya katunan da biyan kuɗi mafi sauƙi da araha ga ’yan Najeriya.