Home Labarai Kungiyar dattawan Arewa ACF ta goyi bayan a binciki Obasanjo kan lantarki

Kungiyar dattawan Arewa ACF ta goyi bayan a binciki Obasanjo kan lantarki

0
Kungiyar dattawan Arewa ACF ta goyi bayan a binciki Obasanjo kan  lantarki

Kungiyar magabatan Arewa ta ACf ta bayyana goyon bayanta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa kwamitin bincike domin bincikar tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo kan irin yadda yayi badakala da kudaden wutarlantarki dalar Amurka biliyan 16.

Kungiyar tace yin wannan binciken ne zai sanya manyan mutane da suke rike da mukamai su shiga taitayinsu wajen alkinta dukiyar al’umma, ba tare da facaka da amubazzaranci ba.