
Daga Hassan Y.A. Malik
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar wasu mutum bakwai a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Gidan-Labbo da ke a gundumar Gidan Goga, cikin karamar hukumar Maradun.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai, NAN, a jiya Lahadi cewa ‘yan bindigar da suka kunna kai ta dajin Malikawa sun farwa mutanen kauyen Gidan-Labbo ne a lokacin da suke gyaran gonakinsu a ranar Juma’ar da ta gabata.
“Muna samun labarin afkuwar lamarin ne bamu yi kasa a gwiwa ba muka aike da jami’anmu inda al’amarin ya faru, inda suka zo mana da gawarwakin mutum bakwai,” inji kakakin ‘yan sandan.
Kakakin ‘yan sanda Shehu ya bayyana cewa tuni dai jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka aike da jami’ansu na musamman don tabbatar da tsaro a yankin.
Muhammad Shehu ya yi kira da al’ummar jihar da su ci gaba da taimakawa jami’an ‘yan sanda wajen aiwatar da ayyukansu ta hanyar tsegunta masu bayanan sirri kan labaran hare-hare da suka samu.
Gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, a ranar Asabar din da ta gabata ya koka kan yadda ‘yan bindigar ke aikewa manoma sakon wasiku, inda suke yi musu kashedi da su guji shuga gonakinsu don yi noma in har suna son rayukansu.
Gwamna Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke kaddamar da sayar da takin zamani ga manoma a garin Nasarawar-Burkullu da ke a karamar hukumar Bukkuyum.
Gwamna Yari ya bayyana wannan barazana a matsayin tashin hankali ga manoman jihar Zamfara, tare da yin alkawarin zai je har Abuja ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma hafsoshin tsaro don neman mafita akan wannan lamari