
Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa, FRSC, reshen jihar Kogi a jiya Talata ta mayarwa iyalin wata da ta yi haɗari a jihar, kuɗi da ya kai Naira miliyan 3.2.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa kudin, mallakar wata Misis Beatrice Ehimare ce da ta yi hatsarin mota a ranar 23 ga watan Janairu, a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja.
Kwamandan Sashen shiyya ta RS8.38 Gegu ne ya gabatar da kudin da aka kwato ga ɗan wacce ta yi haɗarin, David Ehimare.
A yayin gabatar da kuɗin da aka gudanar a Lokoja, kwamandan sashin Kogi, Corps Stephen Dawulung, ya yabawa jami’an da mutane bisa jajircewarsu da kishin kasa.
“Ina so in sake jaddadawa a nan a yau cewa kudiri na ne na ci gaba da aiwatar da aikin ceton rayuka da kare dukiyoyi tare da mafi girman jajircewa, himma da mutunci wanda hukumar FRSC ta shahara da shi.
“A matsayin umarni, muna yi wa Misis Beatrice fatan samun sauki daga raunin da ta samu daga mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Litinin,” in ji shi.